Wani Sanata mai suna Foster Ogola, ya shiga tsundum a cikin harkallar satifiket na kammala jami’a. Sanata Ogola wanda ke wakiltar Bayelsa ta Yamma, ya shiga tsumulmular mallakar takardun karya da ya alakanta daga wata jami’a a Najeriya.
“Shafin san a intanet ya nuna cewa ya na da digirin digirgir daga wata jami’ar Kiristoci, mai suna GMF Christian University. An gano cewa Hukumar Jami’o’i ta Kasa, NUC ba ta yi wa jami’ar rajista ba. Amma kuma shi ya mallaki na sa digirin digirgir din, wato PhD tun cikin 2012.” Haka wani rahoto ya nuna.
Ko a cikin takardun shaidar zurfin ilmin da ya gabatar a Majalisar Tarayya, Ogola ya rubuta cewa ya na PhD daga wannan jami’a. Kuma ya na da digiri na biyu daga Jami’ar Jihar Imo da ke Owerri.
Da aka tsananta bincike, an gano cewa ko lasisi ma gwamnati ba ta bai wa jami’ar wadda ke Lagos ba, inda Ogola ya ce ya yi digirin digirgir a can a cikin 2012.
Da aka tambayi Daraktan Yada Labarai na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, Ibrahim Yakasai, ya bayyana cewa shi bai ma taba jin sunan jami’ar ba sai yau.
Daga nan sai ya bai wa wakilinmu wata mujalla wadda a cikin ta ya nuna sunayen haramtattun jami’o’i har 57 da ba su da rajista a kasar nan. Amma abin mamaki, babu ma ko sunan jami’ar da Ogola ya ce ya yi karatun sa a can.