An kai hari ofishin kamfen din Atiku a Katsina

0

Wasu ‘yan adawar siyasa a jihar Katsina sun kai wa ofishin kamfen din tsohon matimakin shugaban kasa Atiku Abubakar hari dake kan titin Dandagoro, karamar hukumar Batagarawa jihar Katsina.

Wannan abu ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe 8 na dare bayan halartar gangamin jam’iyyar PDP da akayi a garin Katsina.

An tabbatar da cewa babu wanda ya sami rauni ko a wannan hari sai dai an fasa motocin dake ajiye a harabar ofishin.

Bayan haka wanda ya bada gudunmawar ofishin Mas’udu Abdulkadir ya ce wannan aikin na makiyan su ne kuma hakan ba zai sa su karaya ba wajen ci gaba da mara wa Atiku baya.

A karshe kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Gambo Isa yace sun kama mutane uku da ake zargi da hannu a kai harin sannan suna gab da kai su kotu.

Share.

game da Author