Wata mata ta maro wa kan ta tsugune-tashi, yayin da aka gurfanar da ita a gaban mai shari’a, bayan da aka zarge ta da falla wa wani jami’an dan sanda mari.
Matar mai suna Faith Micheal, ta falla wa dan sanda David Akoru mari, shi kuma ya garzaya ya kai rahoto a ofishin ‘yan sanda da ke Karu, Abuja.
Mai gabatar da kara, Vincent Osuji, ya shaida wa mai shari’a a kotun Karu Mai Daraja ta Daya cewa, wadda ta dalla wa dan sandan mari ta aikata laifuka da suka hada da: Hana jami’in tsaro na gwamnatin tarayyar Najeriya gudanar da aikin sa, ci masa zarafi, wulakanta shi, muzanta shi, tozarta shi da kuma yi masa barazana.
Ya kuma ce dukkan wadannan laifukan da ya lissafa kowanen su na zaman kan sa.
An dai yi marin ne tun a ranar 14 Ga Afrilu, 2018. Ita kuma wadda ta yi marin, an gurfanar da ita ne a yau Litinin.
Mai gabatar da kara ya ce ita da wani mutum ne suka ci masa zarafi.
Sai dai ita kuma wadda aka zarga da yin marin, ta bayyana wa mai sharia cewa a mahadar hanyar CBN Junction da ke Karu ne ‘dan sandan ya tare su, a lokacin da wani dan acaba ya goyo ta, inda ya rike dan acaba ya ce sai ya ba shi naira 50.
Har yanzu ‘yan sanda na neman wanda ya taya matar aka mari jami’in su, amma ya tsere babu labari.
Mai shari’a ya bada belin ta a kan naira N20,000, ya umarci su koma kotu ranar 8 Ga Mayu.