Adamawa ta ware naira biliyan 2 don yaki da zazzabin cizon sauro

0

Shugaban kwamitin yaki da zazzabin cizon sauro na jihar Adamawa (SMEP) Isaac Kadala ya bayyana cewa gwamnati ta ware naira biliyan biyu domin kawar da zazzabin cizon sauro a jihar.

Ya sanar da haka ne a taron ranar zazzabin cizon sauro da aka yi a Yola ranar Laraba.

” Duk da cewa jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin dake samun tallafin magungunan don kawar da cutar daga kungiyoyi masu zaman kansu na ciki da wajen kasar nan, haka bai hana gwamnati maida hankali ba wajen ganin ta kara saka kudade don yaki da cutar ta hanyar raba gidajen sauro da magunguna domin mutanen jihar.” Inji Kadala

A karshe kwamishinan kiwon lafiya na jihar Fatima Atiku ta yi kira ga mutanen jihar da su yawaita tsaftace muhallin su.

” Ina kira ga mata masu ciki da su tabbata sun yi gwajin cutar sannan suna shan magani yadda ya kamata.”

Share.

game da Author