A raba aure na da mijina saboda neman saduwa da ni ta baya – Inji Asmau

0

Wata mata mai suna Asma’u Sulaiman ta bukaci kotu dake Magajin Gari a Kaduna ta warware auren ta da mijin ta mai suna Nura Ahmad saboda yawan neman ya sadu da ita ta baya.

Asma’u ta kuma kara da cewa Ahmad kan lakada mata dukan tsiya sannan yana yawan zargin ta da bin wasu mazaje a waje.

” A kwai lokacin da nayi yaji bayan mun yi fada a gida, da kyar aka sasanta mu, amma ina dawowa sai ya fara yi mini zargin wai na zubar da cikin da nake da shi.

Asma’u ta roki alfarmar kotun da a raba auren su, sannan ta ce tana tsoron kada Ahmed ya yafi karfin ta wata rana ya samu ya cika burin sa ta zo ta dauki wani cuta.

Mijin Asma’a, wato Ahmad ya karyata wannan korafi yana mai cewa ba gaskiya ba ce duk abin da da fadi wa kotu.

A karshe Asma’u ta fada wa alkalin kotun Musa Sa’ad cewa tana da shaidar da zata iya gabatar wa a kotu amma sai dai lokacin da take tare da Ahmad har ya nemeta ta baya din bata da shi.

Alkali Musa ya daga karan zuwa ranar 18 ga watan Afrilu domin Asma’u ta sami damar gabatar da shaidar da take da shi a kotun.

Share.

game da Author