Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya nuna takaicin sa dangane yadda ake samun yawaitar rahotannin aikata fyade a jihar, inda har ya yi kira ga duk hukumomin da abin ya shafa da al’umma a hada karfi dokin a magance wannan babbar matsala.
“Rahotannin afka wa mata ana yi musu fyade sai karuwa su ke yi a Gombe; a cikin makonni uku da suka gabata, kusan kowace rana ana samun rahoton aikata fyade sau biyu.
Haka Dankwambo ya bayyana jiya Talata, a lokacin da ya ke karbar bakuncin Kungiyar Lauyoyi Mata ta Duniya (FIDA), reshen Jihar Gombe.
Kungiyar ta lauyoyi matan ta je Gidan Gwamnatin Jihar ne domin kai ziyara ga gwamna a matsayin wani daga cikin tsare-tsaren ta na Makon FIDA na 2018.
Dankwambo ya bayyana abin da ya kira kwatagwalci, inda har aka kama dattijo dan shekara 60 a duniya ya na lalata da yarinya mai shekara hudu a duniya.
Daga nan sai ya ce tilas sai an taya gwamnati yaki da wannan mummunar dabi’a, domin gwamnati ita Kdan ba za ta iya cin nasara ba tare da sa hannun al’umma ba, musamman ma mata lauyoyi, iyaye mata da sauran su.
Daga nan sai ya ce ya umarci shugabannin hukumomin tsaro da su tura jami’an su a makarantun kwana na dalibai mata domin a tabbatar da kyakkyawan tsaro a dukkan makarantun.