Oluwa na masarautar Iwo ya bayyana wa daukacin jama’ar masarautar sa da masarautun yankin kudu maso yamma cewa da ga yanzu ya canza lakanin sarautar sa da daga Oluwo na Iwo zuwa Sarkin Iwo.
Ya ce ya zabi haka ne domin ya bi yadda ake yi a masarautun yankin Arewa.
Oluwo na Iwo, Abdulrasheed Akanbi, ya bayyana canza lakanin sarautar tasa ne da yake nada wani malamin musulunci Yahquub AbdulBaaqi a matsayin wazirin kasar Yarbawa.
Wannan nadin sarauta ya jawo cece-kuce a tsakanin musulman kabilar Yarbawa Inda suka koka kan rashin tuntubar su kafin Olowo din ya nada wazirin kasar Yarbawa.
Sunce kafin yayi haka dole da sai ya tuntube su a yankin kudu Maso Yamma tukunna, amma bai yi haka ba.
Da ya ke kare kan sa Olowo na Iwo, Abdurasheed, ya ce ya canza lakanin sarautar sa ne zuwa Sarki daga Oluwo, saboda rashin hadin kan masarautun kabilar Yarbawa.
” Duk masarautun mu ba su da hadin kai. Daga gulmace-gulmace sai munafurci, da hassada. Amma Idan ka duba yadda masarautun Arewa suke, akwai hadin kai matuka.
” Ba za ka taba ganin wani ya raina na gaba da shi ba, sannan suna da hadin kan gaske. Bayan haka kuma zaka ga su na da dattaku.
” A yankin Yarbawa ne zaka ji babban sarki na kiran wani sarki dan yaudara. Tun ina yaro na ke jin ay da wannan masarautar da wancan ba sa shiri sannan ga maganar tsafi. Idan Kana so ka yi tasiri a yankin mu sai ka dulmiya Kan ka cikin tsafi. Rashin yin haka da nayi ya sa an ki jinina sannan ba a so ana yi da masarauta ta.
” Sannan ina so in gaya wa mutane cewa don kaji ana kiran sarakunan Arewa ‘Amir, wato Emir’ ba Fillanci bane ko Hausa, larabci ne da yake nufin sarki. Saboda haka na dauka nima a kira ni da sarautar. Dama can tarihi ya nuna cewa Oduduwa ma daga kasar Makka ya ke.
Sarki Abdulrasheed ya ce Idan baka da Kudi a yankin kudu, to ba za a dauke Ka a bakin komai ba.
Discussion about this post