A guje shiga shagullan da zai jefa mutum cikin matsanancin damuwa – WHO

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga mutane da su guji abubuwan da zai iya sa su fadawa cikin matsanancin damuwa musamman idan sun tsufa.

Kungiyar ta yi wannan kira ne a shafinta na Tiwita inda ta kara da cewa yin rayuwa na gari zai iya taimakawa wajen guje wa kamuwa da irin wannan cuta.

Bincike ya nuna cewa cutar na iya kama kowa (babba ko yaro) sannan kuma akan sha wuya sosai kafin a gane ko mutum ya kamu da irin wannan cuta.

” Rashin iya gane cutar ya sa matasa musamman masu shekaru 10 zuwa19 daukan ransu, fara shaye shayen miyagun kwayoyi da makananta su.” Cewar WHO.

” Ita dai wannan cuta ta kan kama mutum ne tun yana shekara 14 da idan ba a dauki matakin gaske da wuri ba sai kaga mutum ya fada halin kakanikayi.”

Kungiyar ta ce akan gane cutar ne idan mutum na yawan kin shiga cikin mutane musamman abokanai, rashin samun annashuwa kan abubuwan da akan so a da,rama ko kuma kiba da sauran su.

A karshe kungiyar ta ce za a iya shawo kan cutar ne idan mai fama da ita na yin magana da mutane ko kuma ya nemi likitocin wannan cuta.

Share.

game da Author