Mashahurin Farfesa na Tarihi da Dangatakar Kasa-da-kasa, Akinjide Osuntokun, ya bayyana cewa ba karamin abin takaice ba ne a ce har yau Najeriya ba ta da takamaimen yawan adadin al’ummar ta.
Da yake jawabi a wurin kaddamar da wani littafi da Aisha Osori ta rubuta a Ibadan.
Shehin malamin na tarihi ya bayyana ce duk lalube a duhu ne kawai ake yi, amma a yau babu wanda ya san takamaimen yawan al’ummar Najeriya.
Don haka sai ya yi kiran cewa akwai matukar wajibcin a tattauna batun yawan ‘yan Najeriya, domin a samu yawan adadin kididdigar jama’ar kasar nan, maimakon a ci gaba da tafiya a cikin kirdado, hasashe da hauragiya.
Osuntokun ya kara da cewa a kullum bakin-haure daga Nijar, Kamaru, Jamhuriyar Benin da sauran kasashe sai tutadowa cikin kasar nan suke yi, su na kara mana yawa.
Don haka ya ce akwai bukata ko wajibcin tantance yawan jama’ar kasar nan, inda ta haka ne za a iya gane yawan wadanda ya kamata su cancanci jefa kuri’a.
Ya ci gaba da cewa an dade ana yi wa al’ummar kasar nan lissafin-dawakan-Rano. Don haka ya kamata a tantance.