Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa Najeriya ta yi kaurin suna, kuma sunan kasar ya baci sosai saboda yawan satar kudin gwamnati da aka rika dibgawa a baya.
Haka Trump ya bayyana a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar White House yau Litinin.
Daga nan ya ce Amurka za ta ci gaba da bai wa Najeriya goyon baya domin ganin an kawo karshen wannan musifa ta cin hanci da rashawa da ta addabi kasar.
“Wato Najeriya ta yi kaurin suna sosai wajen cin hanci da rashawa. Na tattauna wannan matsalar da Buhari, kuma mun cimma yarjejeniyar yadda za mu yi wani abu a kan wannan matsalar.”
Bayan da Buhari ya rika nuna farin cikin sa a lokacin da Trump ke magana kan Najeriya, daga baya an tambaye shi shin ko ran sa bai baci ba a lokacin da Trump ya rika tozarta kasashen Afrika baya?
Sai Buhari ya ce shi a ko da yaushe ya na yin taka-tsantsan da wasu rahotannin da kafafen yada labarai ke yayatawa a kan wasu ko a kan sa shi kan sa. Don haka gara kada ya ce komai dangane da irin wadannan rahotannin.
Buhari ya ce ba shi da matsala da dakarun Amurka da ke Najeriya, saboda sun zo ne domin su taimaka a fannin bayar da horo domin a samu nasarar kawar da ta’addanci.
Discussion about this post