Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump ya yaba wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan namijin kokari da yayi wajen ceto ‘yan matan sakandare na Dapchi da a kayi garkuwa da su a kwanakin baya.
Bayan haka Trump ya jinjina wa gwamnatin Buhari bisa himma da ta sa a gaba na ganin ta toshe duk kafar da zai zamo dalilin samun baraka na ci gaba da yawaitar cin hanci da rashawa a kasar.
Trump ya ce Kasar Amurka na farinciki da irin kokari da Buhari ke yi na ganin Najeriya ta farfado ta hanyar inganta tattalin arzikin kasar, tsaro da ayyukan ci gaba.
Idan ba a manta ba Shugaba Buhari yayi ziyarar gayyata ta musamman zuwa Kasar Amurka domin ganawa da shugaban Kasar Donald Trump.
Discussion about this post