Bayan duka da nike sha idan mijina ya sha wiwin sa, har bidiyo ya dauka muna saduwa yana nunawa

0

Wata matan aure a Jihar Oyo, ta shigar da kara kotu tana neman a raba auren ta da mijin ta saboda yada bidiyon su suna saduwa.

Matan mai suna Folasade Olaniyan ta bayyana wa kotu cewa, mijinta ya dauke su a lokacin da suke saduwa da wayar sa sannan ya tuttura wa abokan sa da ‘yan uwanta don ya ci mata mutunci.

Bayan haka kuma tace duk sanda ya kwale da wiwin sa sai ya yi mata dan banzan duka a gidan rannan.

Folasade ta kara da cewa maigidan nata ya dade yana zarginta da kwana da maza saboda kawai tana sana’ar siyar da abinci.

Bayan alkalin kotun ya saurare kukan Folasade, ya warware auren a dalilin wannan korafi sannan kuma da dalilin kin halartar zaman kotun da mijin nata yaki yi.

Share.

game da Author