Gwamnatin tarayya ta sanar cewa zata yi zama na musamman da Kungiyar JOHESU a yau litinin domin tattauna yadda za a kawo karshen yajin aikin da Kungiyar ta fara makonni biyu Kenan.
Gwamnati ta yi wannan sanarwa ne domin ta mayar wa JOHESU martanin tallar da ta sa a jaridar ‘Daily Trust Newspaper’ na ranar Asabar.
JOHESU ta zargi ministan kiwon lafiya Isaac Adewole da yin karfa-karfa da karyata alkawarin da ma’aikatan kiwon lafiya ta dauka game da bukatun kungiyar wanda suka amince a kai a wani zaman da suka yi a shekarar 2014.
Gwamnati ta bayyana cewa wannan magana karya ce domin babu alamun gaskiya a cikin ta.
” Yarjejeniyar da JOHESU ta ke fadi akai shine kudirorin da muka amince a zama da muka yi da su a kwanakin baya’’
Bayan haka Adewole ya ce gwamnati ta kafa kwamitin don duba hanyoyin da suka dacewa don biya musu bukatun su.
Ya kuma ce sun tabbatar wa JOHESU cewa lalle za su kara wa ma’aikatan albashi amma JOHESU ta ki amincewa da wannan magana cewa bukatan su shine gwamnati ta biya su albashi dai dai da likitoci.
” Ko da muka duba tsarin mulkin kasar nan tun daga 1960 zuwa yanzu hakan bai taba faruwa ba sannan faruwar hakan sabawa dokar kasar zai yi.”
A karshe Adewole ya yi kira ga JOHESU da su hakura su janye yajin aikin.