Jiya Lahadi dandazon Kiristoci sun yi zanga-zanga a kan titin jihohin Lagos, Ondo, Osogbo da Ekiti, inda suka rika nuna zazzafan fushin su kan gwamnatin Muhammadu Buhari, saboda sakacin da gwamnatin ta yi na bari kashe-kashe a yankuna daban-daban na kara kamari da muni a kasar nan.
Sun kuma dauki alkawarin cewa muddin gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta kawo karshen wannan kashe-kashe ba, to za su kayar da ita a zaben 2019.
Dama dai tun a ranar Laraba da ta gabata ne Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, Olasupo Ayokunle, ya umarci daukacin Kiristocin kasar nan da a fita a nuna bacin rai da damuwa dangane yadda ake yawan kashe-kashe a kasar nan, musammnan wadanda aka kashe har da limaman su biyu da wasu masu bauta 15 a cikin coci a jihar Benuwai.
Da yawan wadanda suka yi zanga-zangar sun nuna cewa an zabi Buhari a bisa kyakkyawan zaton zai kawo karshen kashe-kashe da zubar da jini a kasar nan.
Sun nuna takaicin su yadda kashe-kashen kabilanci, rikicin Fulani da makiyayya da kuma yawan sacewa da garkuwa da mutane ke ta kara ruruwa a zamanin wannan gwamnati.
Yawancin wadanda suka yi zanga-zangar ‘yan darikar Katolika da Baptist ne da kuma wasu dariku daban-daban.