BOKO HARAM: Gwamnatin Obama ba ta bai wa Najeriya goyon bayan kirki ba – Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa ba ta samu taimako ko goyon baya na a-zo-a-gani daga gwamnatin Barack Obama, wajen yaki da Boko Haram ba.

Kakakin Yada Labaran Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya yi wannan hasashen a jiya Lahadi a Washington DC, babban birnin kasar Amurka a lokacin da ya ke tattaunawa da ‘yan jarida.

A yau ne dai Buhari zai gana da shugaba Donald Trump na Amurka a Fadar White House.

Garba Shehu ya ce tattaunawar ta su za ta karkata ne kan matsalar tsaro, musamman yaki da ta’addanci.

Ya ce dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka ta kara karfi tun bayan hawan Trump kan mulki.

Ya ce a matsayin Buhari wanda shi ne shugaba na farko a wannan shiyya ta Afrika da zai gana da Trump bisa gayyatar da ya yi, masa, hakan na nuni da irin yadda Najeriya din ke da muhimmanci.

Ya ce kuma akwai tawaga guda biyu bayan batun tattauna tsaro, akwai kuma tawaga ta ‘yan kasuwa da masu masana’antu, inda za a tattauna batun zuba jari domin kara habbaka tattalin arziki a kan turbar dimokradiyya.

Shehu ya ce gaba da cewa akwai wasu tarnaki da dama da aka cire a karkashin mulkin Trump, wadanda hakan ne ma ya kara saukaka huldar cinikakkya a tsakanin kasashen biyu, musamman bangaren matsalar tsaro.

Shehu ya nuna farin cikin yadda wasu ‘yan Najeriya mazauna Amurka suka fito dauke da kwalaye har zuwa Blair House, masaukin Shugaba Buhari, suka yi masa zanga-zangar nuna amincewa da goyon baya kan yadda ya ke yaki da cin rashawa a Najeriya.

Shugaban gungun mutanen mai suna Wale Adewoye, ya ce sun je ne domin su nuna wa Buhari goyon bayan su.

A cewar sa, sun fahimci lallai an tabka barna a Najeriya, wadda ba su ankara da irin munin ta ba, sai da Buhari ya hau mulki aka rika fallasawa tukunna suka ankara.

Share.

game da Author