Mahara sun kashe mutane 8 a Birnin Gwari

0

Al’ummar Birnin Gwari sun afka cikin halin rudu da jimami bayan mahara sun kashe wasu masu hakar ma’adinai su 8 a ranar Asabar da ta gabata.

Rahotanni sun ce kisan ya afku ne da misalin karfe 11 na rana.

An ce maharan sun kutsa a cikin dajin da mahaka ma’adinan ke aiki can kusa da tsohon garin Birnin Gwari, inda nan take suka bude musu wuta, suka kashe su.

Har yanzu dai babu takamaimen yadda abin ya faru, domin baya ga wadanda suka rasa ran su, wasu da dama kuma sun tsira da raunuka a jikin su.

Wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa daga cikin wadanda aka kashe din, har da surikin sa mai suna Magaji Danjuma.

“Suriki na Magaji Danjuma na daga cikin wadanda aka kashe. Shi kona shi ma suka yi da wuta, ya babbake. A haka aka kawo mana gawar sa”.

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kaduna, Austin Iwar ya tabbatar da faruwar lamarin a wayar tarho da aka yi magana da shi.

Share.

game da Author