‘Yan daba sun fatattaki Sanatan Kaduna a wajen taro

0

Wasu gungun ‘yan daba sun tarwatsa taron siyasa da sanata Suleiman Hunkuyi, mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar Dattawa, ya shirya a garin Kaduna.

Sanata Hunkuyi tare da makarraban sa sun halarci wani taron wayar wa ‘ya’yan jam’iyyar kai ne da yi musu gargadi da kada su bari ayi musu karfa-karfa a zaben wakilai da za a yi a jihar ranar Asabar mai zuwa.

Jim kadan bayan sun halarci wurin wannan taron, sai gungun matasa dauke da makamai suka far wa wannan wuri suna ife-ife suna fadin ” Kaduna sai Uba Sani, Kaduna sai El-Rufai” .

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ne ta ruwaito wannan labari in da ta kara da cewa mutane da yawa sun sami rauni a wannan yamutsi sannan dukkan su na kwance a asibitin Garkuwa da Barau Dikko a na duba su.

Da ya ziyarci asibitin domin duba’yan jam’iyyar da ‘yan daban suka illata, sanata Suleiman Hunkuyi ya ce wadanda suka yi haka sun yi ne ganin cewa ya zame musu haki a ido, sannan ta haka ne kawai za a iya muzguna masa.

Hunkuyi yace ba taron siyasa suka zo yi ba, sun zo ne su gana da ‘yan jam’iyyar su na APC sannan su gargade su cewa kada su bari a rude su ko ayi musu karfa-karfa a wajen zaben wakilai da za ayi a jihar.

Rahotannin sun nuna cewa shi kansa shugaban Kamfanin ‘ATAR Communication’ Tijjani Ramalan ya sha da kyar ne domin an rorrotsa masa motocin sa.

Da aka nemi ji daga bakin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Austin Iwar, ya tabbatar da cewa lallai sanata Suleiman Hunkuyi ya sanar wa ‘yan sanda abin da ya faru, bayannan Iwar bai ce komai ba.

Share.

game da Author