Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana kan wasikar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya aika masa, inda ya nuna cewa bai cancanci tsayawa takara a karo na biyu na wato a 2019, don haka ya sauka idan ya kammala zangon sa na farko.
Obasanjo dai ya rubuta wasikar tun cikin watan Janairu, amma tun daga lokacin Buhari bai ce komai ba, sai wannan karon.
Wasikar dai doguwa ce mai dauke da shafuka har 13. Kafin sannan kuwa, Obasanjo ya goyi bayan zaben Muhammadu Buhari a 2015.
Kuma duk da cewa ya yi shugabancin kasar nan har sau biyu a karkashin PDP, sabanin da ya shiga tsakanin sa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sa har ya kekketa takardar sa ta shaidar dan jam’iyyar PDP a cikin 2014.
A lokacin da ya ke bayani a Bauchi wurin taron liyafar cin abinci da aka shirya domin karrama shi, shugaba Buhari ya ce bai yi niyyar cewa komai ba, amma dai a lokacin Ministan Yada Labarai ya nuna muhimmancin maida amsa, inda aka yi yarjejeniyar cewa a maida amsa ta hanyar lissafa muhimman ayyukan da gwamnatin APC ta gudanar kawai, ba tare da maida martani ko rubuta sunan Obasanjo a cikin wasikar ba.
Buhari ya ce ya umarci Lai kada ya maida wa Obasanjo martani, saboda dalilai biyu: “Na farko shi yaro ne sosai ga wanda ya rubuto min wasikar, kuma yaro ne sosai ga ni da aka rubuta wa wasikar.”
“Da Lai Mohammed ya shigo ofis di na, sai na ce ya fita waje. Sai ya ce min a’a shi fa ba zai fita ba. Ya ce saboda me? Ya ce ya na so na yi masa uziri, na saurari abin da zai fada. Sai ya ce min zai maida wa Obansanjo amsa kawai ta hanyar tunatar wa ‘yan Najeriya matsayin da Najeriya ta ke ciki a lokacin da muka hau mulki, matsayin da muke ciki a yanzu da kuma ayyukan da muka yi da abin da ke hannun mu.
“Nan take na amince da shawarar Lai, muka tsaya a haka din. Kuma na gane cewa ‘yar tankiyar da na yi da shi, lallai ya fi ni gaskiya, domin iya wadanda na yi magana da su bayan Lai ya yi martanin, sun shaida min cewa ya yi magana mai muhimmancin gaske.
“Don haka ina murna da irin gagarimin kokarin ayyukan da jam’iyyar mu APC ta aiwatar.”
Buhari ya kuma bayyana yadda wasu makusantar siyasar sa da suka yaudare shi, wanda hakan ne ya sa shi neman wata sahihiyar jam’iyyar da zai shiga domin ya ceto kasar nan.
“Bari ma na dan bada wani tarihi na abin da ya faru can baya, domin jama’a su yi hukunci da kan su. A lokacin da mu na ANPP, na shiga zaben takarar fidda gwani kuma na yi nasara a bisa tsarin ingantaccen zabe. Na kuma je kotu har sau uku ko sau hudu duk don saboda ina ganin cewa a shirye na ke na zama shugaban kasa. Amma me zai faru, wanda ya kamata a ce shi ne ya zama mataimaki ne, sai ya bada kai bori ya hau, gwamnatin da muke adawa da ita ta ba shi mukami, kuma ya karba.”
“Shi ma shugaban jam’iyya da mataimakin sa duk suka dunguma cikin gwamnati, aka ba su mukamai. Abin haushi a lokacin fa duk ina kotu ana fafata shari’a. Dalili kenan na fice daga jam’iyyar muka kafa CPC. Da jam’iyyar adawa ba ta karbe mulki daga PDP ba, to da yanzu kasar nan ta balbalce kawai.”