Gwamnonin jam’iyyar APC, wadanda dama can akasarin su jiga-jigan jam’iyyar PDP ne, za su yi abin nan da Bahaushe ke cewa, ‘gida bai koshi ba an ba daji’, inda za su kashe naira bilyan 6 domin gudanar da tarukan gangamin jam’iyya da kuma zaben shugabannin jam’iyyar.
Gwamnonin za su yi wannan bushasha da kudin ne, duk kuwa da irin dimbin kudaden bashin da ma’aikatan jihar ke bi wajen kasawa ko kin biyan albashi, kudaden fansho da sauran hakkokin da jama’a ke bin su.
PREMIUM TIMES ta gano cewa gwamnonin 24 kowa zai bayar da gudummawar naira milyan 250 daga cikin asusun hakkin al’ummar jihar sa domin a kashe a wurin gangami da zaben shugabannin jam’iyyar.
17 daga cikin gwamnonin 24 dai duk gyauron jam’iyyar PDP ne, wadanda suka fice daga inuwar lema, suka damka wa talakawa tsintsiya, su kuma suka shara musu tulin kuri’u a karkashin APC, da nufin tabbatar musu da canji.
APC ba ta sa ranar gudanar da taron ba, amma dai ta hakkake cewa a cikin watan Mayu mai kamawa za a gudanar da shi.
Gwamnonin da za su bayar da gudummawar naira milyan 250 daga aljihun asususn jihar sun hada da:
Bindo Jibrilla (Adamawa), Mohammed Abubakar (Bauchi), Samuel Ortom (Benue), Kashim Shettima (Borno), Godwin Obaseki (Edo), Rochas Okorocha (Imo), Abubakar Badaru (Jigawa), Nasir El-Rufai (Kaduna), Abdullahi Ganduje (Kano) Aminu Masari (Katsina), Abubakar Bagudu (Kebbi) da Yahaya Bello (Kogi).
Sauran sun hada da: Abdulfatah Ahmed (Kwara), Akinwunmi Ambode (Lagos), Umaru Tanko Al-Makura (Nasarawa), Abubakar Bello (Niger), Ibikunle Amosun (Ogun), Oluwarotimi Akeredolu (Ondo), Rauf Aregbesola (Osun), Abiola Ajimobi (Oyo), Simon Lalong (Plateau), Aminu Tambuwal (Sokoto), Ibrahim Geidam, (Yobe), da Abdulaziz Yari, (Zamfara).
Abin mamaki dangane da wannan karo-karon Makudan kudade da za su yi, shi ne tun a cikin watan Fabarairu da ya gabata gwamnoni 23 daga cikin 24 din nan suka shiga jirgin rikicin rashin biyan albashi, inda ya sauke su a cikin tashar rigima da kunyoyin ma’aikata da kwadago na jihohin su.
Jihar Lagos ce kadai ke iya biyan hakkin ma’aikata daidai yadda ya kamata, kamar yadda Kungiyar Ma’aikata ta tabbatar.
Sauran jihohin daga masu yi wa ma’aikata biyan-bashin-daddawar-kauye, sai masu sayar da awakin Jatau su biya bashin Ja’e, wanda suka sayar da dabbobin sa amma ba su biya shi a lokacin ba.
Gwamnoni da yawa daga cikin su ana bin su bashin kudaden fansho na wata da watanni. Wasu ma kamar yadda bincike ya tabbatar, na shekaru da dama ake bin su bashi.
Tun da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki gwamnoni ke fama da buga-bugar kasa biyan hakkin ma’aikata, duk kuwa da naira tiriliyan 1.9 da ya ba su a cikin shekarun nan uku, wadanda ba su cikin kudaden da gwamnatin tarayya ke rabawa ana ba su a duk karshen kowane wata.
Da yawan su ba su gabatar da ayyukan a-zo-a-gani a jihohin su ba. Yayin da ake kara tula musu kudaden, a lokacin wasun su da dama ke kara haurawa kasashen waje su ciwo bashi.
Daya daga cikin gwamnonin ya je kasar China sau shida a cikin shekara uku, amma akwai karamar hukumar da bai taba sa kafar sa ba, tun da ya hau mulki har yau.
Ko kwanan nan Majalisar Dattawa ta taka wa Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai burki daga ciwo wa jihar Kaduna bashin dala milyan 350. Yayin da shi kuma ya ce ba wanda ya isa ya hana shi ciwon bashin.
Akasarain irin wadannan bashi dai ba gwamnan da ya ciwo ba shi ke biya ba.
Sai wata gwamnanti ta hau bayan ya sauka, sannan ruwan bashin zai kulle gwamnan da al’ummar jihar ciki.
Wani abin mamaki kuma shi ne da yawan jihohin ba su iya tara kudaden haraji na a zo a gani, kowace da kudin man fetur ta dogara. Misali, jihar Benuwai za ta kamfaci naira milyan 250 ta bayar domin taron gangamin jam’iyya, alhali kuma kudin shigar da ta ke tarawa a duk wata bai wuce naira milyan 250 ba.
Wannan ne Hausawa ke cewa ‘indararo ba ka ba gida sai titi.’