Yadda Gwamnonin APC suka kusa ba hammata iska a wurin taro

0

An yamutsa gashin-baki sosai, an kuma tayar da jijiyoyin wuya, jiya Alhamis a wurin taron gwamnonin jam’iyyar APC, wadanda suka taru domin tattauna wasu muhimman batutuwan da ya shafi jam’iyyar, musamman dangane da shugabancin jam’iyya.

Wasu da suka shaida abin da ya faru a wurin taron, sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa gwamnonin sun tattauna batun ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar na kasa, inda a kan tattauna na su batun ne taron ya yi zafi, har sai da wadanda suka kai zuciya nesa suka shiga tsakanin wasu hasalallun cikin su.

Mutane biyu ne ke takarar shugabancin jam’iyyar na kasa – wato John Odigie-Oyegun wanda wa’adin mulkin sa zai kare a karshen watan Yuli, amma aka sake ba shi damar sake tsayawa takara, da kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole.

Majiya ta ce ana tsakiyar taro ne wanda ba a bar manema labarai sun shiga ba, sai rincimi ya harde a tsakanin gwamnonin kan batun taron gangamin jam’iyyar da za a gudanar nan gaba.

PREMIUM TIMES ta ji cewa jam’iyyar na shirin tura wakilai su sa-ido kan yadda za a yi zaben, amma kowane a jihar da ba ta sa ba za a tura shi.

Dama kuma su ma gwamnoni an amince su tura sunayen wakilan da suke so su zama wakilai a wurin zabe.

Wato a nan, ana nufin wakilin da ya fito daga Gombe, zai iya zama jami’in sa-ido a Katsina ko jihar Sokoto.

An ce a tura dukkan sunayen a babbar hedikwatar jam’iyyar a Abuja.

AKEREDOLU DA OKOROCHA KUSA RABA RANA

PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa wannan tsari bai yi wa wasu gwamnoni dadi ba, musamman, Rochas Okorocha, Gwamnan Jihar Imo.

Gwamnan ya ce bai yarda a tura jami’ai ko wakilan wasu jihohi a jihohin da ba na su ba.

Ya yi barazanar cewa zai sa kafar wando daya da duk wanda ya tura wakilan jihar Imo wata jiha.

Jin haka, sai gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya yi caraf, ya ce Okorocha shirme da bankaura kawai ya ke yi, domin ba abin da zai iya yi, tunda ba shi ne kan gaba da kowa a cikin jam’iyyar APC ba.

Ya ce duk abin da jam’iyya ta gindaya, to ya zauna, babu mai tayar da shi.

Har ya kai ga kalubalantar Okorocha da ya yi duk irin dabancin da ya san zai iya idan ya isa.

Ganin abin ya kai Akeredolu da Okorocha tayar da jijiyar wuya, sai sauran gwamnoni suka yi sauri suka ba su hakuri don kada su kai ga cin kwalar juna.

TSAKANIN EL-RUFAI DA AJIMOBI

Can kuma bayan an ci gaba da taro, sai Okorocha ya kara kunno wata wutar, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a zabi Adam Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyya.

Ya ce Buhari ya fadi haka a lokacin da suka yi ganawa da shi a ranar Alhamis din, kafin su kai ga shiga taron da suke tattaunawar.

Shi kuma Gwamna El-Rufai, wanda dama ya na cikin gwamnonin da suka ziyarci Buhari a ranar, sai ya yi zambur ya karyata Okorocha.

El-Rufai ya ce abin da aka zartas shi ne shugaba da gwamnoni ba za su bada fifiko kan kowane dan takara ba idan kowanen su ya je kamfen.

Rufe bakin El-Rufai ke da wuya, sai gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, surukin Gwamna Abdullahi Ganduje, ya nuna El-Rufai ya ce masa haba Malam, ya za ka yi wa mutane baki-biyu?

Kafin wannan taron, kowa ya hakkake cewa El-Rufai ya na bangaren Oyegunn ne. Shi kan sa Oyegun din ya yi amanna cewa duk lokacin da Buhari ya rufe kofa tare da El-Rufai, to gwamnan na share masa hanya ne a wurin shugaban kasa.

Amma nan take sai Ajimobi ya nuna El-Rufai ya ce ai da shi suka je gidan Oshiomhole ranar Talata da dare. To ya na mamakin yadda ya ke nuna kamar ya na goyon bayan Oyegun a sarari.

Ajimobi ya ce a gaban sa El-Rufai ya yi wa Oshiomhole mubayi’a, kuma ya tabbatar masa da cewa shi zai yi nasara a wurin gangamin taron zabe.

Dukkan ‘yan takarar biyu dai daga jihar Edo suka fito.

Daga kuma yarjejeniyar da aka yi bayan an sauke shugabannin a farkon wannan watan, an amince cewa ‘yan takarar kowane mukami su fito daga jihar wanda aka sauke.

Yayin da Oshimhole ya dade ya na neman wannan shugabanci na jam’iyyar APC, kuma ya samu shiga sosai, alamomi na cewa akwai wasu gwamnonin da ba su amince da shi ba, saboda ana zargin cewa dan-gaban-goshin Bola Tinubu ne.

An ce dalili kenan gwamnoni irin su Akeredolu tun yanzu suka daura banten kokawar hana shi zama shugaban jam’iyya a ranar gangamin taron APC.

Lokacin da PREMIUM TIMES ta buga wayar Kakakin APC, Bolaji Abdullahi bai dauki wayar sa ba, balle a ji ta bakin sa.

Share.

game da Author