Kakakin gwamnan jihar Sokoto, kuma fitaccen dan jarida, Imam Imam ya rasu a Abuja, bayan yar gajeruwar rashin lafiya da yayi fama da shi.
Imam fitaccen dan jarida ne da ya fara aiki jarida a New Nigeria dake Kaduna.
Wani makusancin sa ya shaida mana cewa za a yi jana’izar Imam a masallacin Annur dake Abuja da karfe 1: 30 na ranar yau.
Allah Ya ji Kan sa. Amin.