RUGUNTSUMI: Jiga-Jigan Jam’iyyar PDP sun koma APC

0

Shugabannin jam’iyyar PDP dake shugabancin jam’iyyar a jihohi da wasu gagga-gaggan ‘yan jam’iyyar PDP sun canza sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Dukkan su dai sun yi mulki ne kuma magoya bayan tsohon shugaban jam’iyyar Ali Modu Sherrif kafin Kotu ta tsige shi.

A taron karbar su da akayi a hedikwatar jam’iyyar dake Abuja, Shugaban jam’iyyar John Oyegun ya yi wa bakin lale marhaban sannan ya ce wannan babbar kamu ne jam’iyyar tayi.

Cikin wadanda suka halarci bukin wankan akwai gwamnonin Kaduna, Kogi da Kano sannan sakataren gwamnatin tarayya ya halarci taron. Sannan Gbemisola Saraki da Teslim Folari suna daga cikin wadanda suka canza shekar.

Share.

game da Author