Dakarun tsaron Najeriya sun fatattaki Boko Haram bayan an dauki awowi ana batakashi da ‘yan kungiyar.
Boko Haram sun far wa unguwar Polo Jidari dake Maiduguri da safiyar Alhamis din yau in da mutanen unguwar Kaf su fice daga gidajen su tsoron kada a kashe su.
Shugaban rundunar Operation Lafiya Dole’ Nicholas Rogers ya bayyana cewa tare da hadin guiwar jami’an tsaro na ‘civil Defence’ na sa kai da sojin saman Najeriya, sun sami nasarar fatattakar su gaba daya.
Sannan yayi kira ga mazauna wannan unguwa da su dawo gidajen su su ci gaba da harkokin su.
” Ina kira da mazauna wannan unguwa da su dawo su ci gaba da harkokin su sannan ina rokon su da su tona duk wani bakon fuska da su ka gani a unguwar.
Rogers ya ce dakarun su sun fantsama daji don bin sahun wadannan miyagun mutane.