Jam’iyyar APC a jihar Barno ta karyata rade-radin da akayi ta yadawa cewa wai tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ali Modu Sherrif zai canza sheka zuwa Jam’iyyar a yau.
Shugaban jam’iyar na jihar Barno Ali Dolori ya karyata wannan zance inda ya ce wasu ne kawai suke fesa wannan zance domin su hargitsa shirin zaben wakilan jam’iyyar da ake shirin ya a jihar.
Dalori ya ce kowa ya san yadda a ke shiga jam’iyya, ” A jam’iyyar ta APC mun san yadda ake shiga jam’iyya, dole sai ka koma mazabar ka ka yi rijista kafin ka zama dan jam’iyya. Ko kuma kayi ta yanar gizo. Idan ba ta wannan hanyoyi ba babu ta yadda zaka iya zama dan jam’iyya.
” Wasu ne kawai ke ta yada wannan zance domin kawo rudani a jam’iyyar APC na jihar wanda ba za su sami nasara kan haka ba. Zamu mu dakile duk wani bita da kulli da wani ke shiryawa don tada da fitina a jihar Barno.
Idan dai ba a manta ba tun bayan tallata wa duniya da labaran jaridun kasar nan suka yi cewa jam’iyyar APC za ta wanke Ali Modu Sherrif a hedikwatar jam’iyyar yau cewa zai canza sheka daga PDP zuwa APC hakan dai bai yiwu ba.
Bayan manema labarai sun taru a ofishin jam’iyyar dake Abuja, tun da asubahin farko zuwa karfe 12 na rana da aka ce zai iso hedikatar jam’iyyar domin ganawa da shugabannin APC da sauran ‘ya’yan jam’iyyar, karshen ta dai sai dai kowa tattara komatsan sa yayi kara gaba.
Daga baya sai kakakin jam’iyyar Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa ba a hedikwatar jam’iyyar ne ake ba da katin zama dan jam’iyya ba.
” Duk mai bukatar ya shigo jam’iyyar APC, a mazabar sa zai karbi katin shiga ba hedikwatar jam’iyyar ba.”