Shugaba Muhammadu Buhari ya samu damar sake fita kasar waje, inda ya furta magana wadda ke da matukar muhimmanci dangane da tattalin arziki da kuma al’ummar kasar nan. Mai yiwuwa irin yadda aka rika maida masa martani, shi a zuciyar sa ba kamar yadda aka fahimce shi ya ke nufi ba.
A yau dai matasa sun dirar masa, a kullum sai caccakar sa suke yi a soshiyal midiya, jin yadda ya bayyana su a matsayin sangartattun jahilai masu zaman dirshan, ba su komai sai jiran a samar musu ilmi, lafiya da gidaje kyauta, saboda kawai su na kallon Najeriya kasa ce mai arzikin danyen man fetur.
Tabbas tunda ana cikin shekarar da zabe ke karatowa, za a yi tsammani masu adawa su nuna fushin su kan shugaban kasa.
Su kuma hadimai da masu kare jawabin da Buhari ya yi, sun yi ta kokarin su nuna cewa ai ba kudin goro Buhari ya yi wa matsa ba, wasu daga cikin su ya tsame ya yi magana a kan su. Sannan kuma su a na su tunanin, don me za a tika cewa Buhari ya kira matasa raggaye, alhali kuwa a cikin jawabin na sa bai ambaci kalmar raggaye ba.
Ko ma dai me kenan, tunda Buhari ya ce matasan su na zaune ba su aikin komai su na jiran na-kyauta, ai kalmar raggaye ta fito fili kenan. babu wani kanikanci da masu dadin-baki za su iya yi, domin su tayar da mummunar komadar da kalaman Buhari zuka yi.
Ya kamata Shugaban Kasa ya fara koyon mulki da bakin sa, kafin ya fara koyo da hannu ko da umarni. Bai kamata ya maida dandalin jawabi a kasar waje wani wurin farke wa kasar sa laya da tozarta ‘yan kasar ba. Ko ma dai me kenan, furucin da Buhari ya yi, ya nuna cewa matasa su ma su na da bakin ba shi amsa, kuma har yanzu ba su daina ba shi amsar haushin sa da suke ji ba.
Duk da haka, ya na da kyau a duba wasu batutuwa guda biyu dangane da kalaman Buhari, wadanda sun danganci tattalin arziki. Batutuwan kuma su ne yawaitar matasa marasa aikin yi, sai kuma dandazon yaran da suka gama firamare da sakandare. Shin mene ne makomar su?
Kashi 80 cikin kashi 100 na al’ummar Najeriya, ‘yan kasa da shekar 40 ne. Sama da kashi 3 na ‘yan kasa da shekara 35, su na zaune ba su je jami’a ba. Kashi 2 bisa 3 na ‘yan kasa da shekaru 40 ba su da aikin yi ko sana’ar dogaro. Kamar yadda kididdigar Satumba, 2017 ta nuna. Kashi 73.5 kuma ayyukan da suke yi bai ishe su dogaro da kan su ba, sun a dai yi ne kawai maganin zaman-banza.
Idan aka dubi batun ilmi da ya yi magana kuma, za a ga cewa kididdiga ta nuna matasa masu shekaru 15 zuwa sama, kusan sun kai kashi 51.1 wadanda ke da ilmi. Daga shekara 15 zuwa 24 kuma wadanda suka cancanta a ce sun samu aiki sun kai kashi 66.4, ko suna aiki saboda cancantar su, amma kuma babu aikin.
Sai a sake dubawa kuma, shin tattalin arzikinmu ya samar wa masu neman guraben aiki samun aikin? Shin wadanda ke neman aikin su ne ake bai wa aikin? Ta ina masu neman aiki hajaran-majaran suka zauna ba su karbi aikin da ba su son yi ba?
A matsayin yadda tattalin arzikin mu wanda ya shafe shekara-da-shekaru ya na walagigi, a yanzu ba zai iya samar da aiki ga dandazon tulin matasan da suke kammala karatu a kowace shekara ba.
A gefe daya kuma, masu bai wa matasa shawarar su fantsama cikin kananan sana’o’i musamman na hannu kamar noma, sun kasa fahimtar cewa yanayin kasar nan ba zai iya bai wa matasa damar yin wani tasiri a irin wadannan sana’o’i ba.
A gaskiya akwai babban kalubale wajen tabbatar da cewa babban jarin da kasar nan ke tutiya da shi, wato matasa, sun zamanto su na samun damar shiga gaba, wajen harkoki da fannonin ciyar da tattalin arzikin kasa gaba, kamar yadda duniya ke ci gaba a halin yanzu.
Yayyin da wannan furuci da shugaban kasa yay i ke ta haifar da rura wutar zafafan ra’ayoyi, to a gefe daya ya na kara murja zaren zabe mai zuwa, za a iya cewa Buhari ya taimaka wajen farkar da mu domin mu tashi mu tantance wace alkibla ce mafi muhimmanci da tattalin arzikin kasar nan zai fi bai wa muhimmanci? Kuma ta yaya za a aiwatar da hakan a kan hanya madaidaiciya.
Discussion about this post