ANA WATA GA WATA: Sanatoci sun yi kira da a fara shirin tsige Buhari

0

A safiyar Alhamis din yau ne wasu gungun sanatoci suka yi kira da majalisar dattawa da ta fara shirin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda karya dokar kasa da yayi.

Sanata Matthew Uroghide, daga jihar Edo ne ya jagoranci wannan muhawara a zauren majalisar, inda ya ce kudin da shugaba Buhari ya cira daga asusun kasa wai don siyan makamai ba tare da sanin majalisa ba laifi ne sannan karya dokar kasa ne da ya yi daidai da a tsige shi.

“Idan ba a manta ba Shugaba Buhari ya cire zunzurutun kudi sama da dala miliyan 400 domin siyan makamai batare da majalisar kasa ta sani ba ko kuma ta bashi daman yin haka wanda saba wa doka ce kuma daidai yake da a tsige irin wannan shugaba.” Inji sanata Matthew Uroghide.

Share.

game da Author