Kawar da zazzabin cizon sauro ne mafita a gare mu – Wakilin WHO

0

Masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya sun yi kira ga kasashen duniya da su kara maida himma don kawar da zazzabin cizon sauro a kasashen da ke fama da cutar.

Gwanayen sun yi wannan kira ne a taron ranar zazzabin cizon sauro da ake yi ranar 25 ga watan Afrilun kowace shekara.

” Yin wannan kira ya zama dole ganin yadda cutar ke kara yaduwa a kasashen duniya”

” Bincike ya nuna cewa mutane sama da miliyan 216 a duniya ne suka kamu da cutar a shekarar 2016 sannan kashi 91 bisa 100 cikin wadanda suka rasu mutanen kasashen Afrika ne.”

” A yanzu haka kashi 27 bisa 100 na mutane a Najeriya na fama da cutar sannan gwamnatin kasar bata yi wani abin a zo – a gani ba zuwa yanzu.”

A karshe shugaban kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) Tedros Ghebreyesus a madadin sauran masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya ya bayyana cewa dole ne fa sai an dawo da aga rakiya halin ko in kula da ake nuna wa game da cutar an hada karfi da karfe sannan za a iya kau da shi kwata-kwata a kasashen da ke fama da cutar. Idan ko ba haka ba za a kwan ciki.”

Share.

game da Author