Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa Kennedy Idirisu ya bayyana cewa rikici ya barke a tsakanin kabilun Ebira da Bassa dake zama a kauyen Ugya a karamar hukumar Toto a jihar.
Ya sanar da haka ne da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Lafia inda ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga wanda akeyi a tsakanin kabilun biyu a jihar Kogi.
Ya kuma ce duk da cewa basu da masaniya kan adadin yawan mutanen da suka rasa rayukan su a rikicin sai dai ya tabbatar wa manema labarai cewa jami’an tsaron ba za suyi kasa-kasa ba wajen bankado duk wanda ke da hannu a wannan aika-aika.
A karshe Idirisu ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jiharAhmed Bello ya bada umurnin karfafa tsaro a yankunan Sabon Karu da Keffi.