Majalisa bata isa ta canza yadda za ayi zabe ba – Kotu

0

Babban Kotu dake Abuja ta bayyana cewa dokar kasa bata ba majalisar kasa ikon iya canza fasalin zabe a kasar nan.

Alkalin kotun , mai shari’a Mohammed Ahmed ne ya yanke wannan hukunci a zaman kotun yau a Abuja.

Mai shari’a Ahmed ya ce doka ta yardar wa hukumar zabe ne kadai ta shirya zabe da duk wasu abubuwan da ya shafi harkar zabe a kasar nan amma babu wanda doka ta amince wa ya shirya ko ya canza jadawalin zabe a kasar nan.

Ya ce dole su kan su majalisa su bi wannan doka kamar yadda take a kundin tsarin mulkin Najeriya.

” Idan har majalisa na so ta sami irin wannan dama dole ne sai an yi wa kundin tsarin mulki garambawul.”

Jam’iyyar Accord ne ta garzaya kotu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa ya saka hannu a kudirin majalisar da ya nemi a canza yadda a ayi zabe a 2019.

Tuni dai Buhari yayi watsi da wannan zance sannan ya maidpo wa majalisa wadannan kudirori da basu saka hannu ba.

Share.

game da Author