Dole kasashen Afrika su mai da hankali wajen kawo karshe matsanancin yunwa da yara ke fama da shi

0

Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga kasashen Afrika da su nema wa kasashen su mafita game da illolin da matsinacin yunwa ke yi wa yara da illar da cika cika ciki fam ke yi wa yara a kasashen su.

Kungiyar ta yi wannan kira ne ganin cewa akwai shiri na musamman domin samar da kiwon lafiya mai nagarta a kasashen zuwa shekarar 2030.

” Bincike ya nuna cewa yara miliyan 59 ne ke fama da matsinacin yunwa a kasashen Afrika da ke han su girma yadda ya kamata sannan wasu miliyan 10 na fama da ciwon kiba saboda yawan cin abinci.”

Share.

game da Author