Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa shi a rayuwar sa ba ya na neman shugabancin kasa bakin-rai-bakin-fama ba ne, kamar yadda wasu mutane ke masa mummunar fahimta.
“Ai da bakin rai bakin fama na ke neman shugabanci, da ban janye na bar wa M.K.O Abiola takara a 1993 ba.” Inji shi.
Atiku ya yi wannan kalamai ne yau Talata da safe a cikin wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC.
Ya ce idan da mutane za su bibiyi tarihin siyasar sa, to za su yi masa hukunci da cewa shi ba mutum ba ne mai neman mulki ido-rufe.
Ya ce ko a 2007 da ya tsaya takara da Obasanjo, ai ya yi ne domin ya nuna wa duniya cewa ya na da dama da ‘yancin tsayawa takarar shugaban kasa.
Ya ce tun lokacin da ya ke tsayawa takara, ai sau daya ne kawai ya fito takarar shugaban kasa a matakin karshe, sauran lokutan duk a zaben-fidda-gwani kawai ya ke tsayawa, ba a kai ga tsayar da shi a matsayin gwanin jam’iyya.
“Kuma da na so ai da na zama shugaban kasa a cikin 2003, a lokacin da kusan dukkan gwamnoni suka mara min baya, suka ce ni suke so, amma ban tsaya ba, Obasanjo ya sake tsayawa ya yi nasara.”
“Amma dai a matsayi na na wanda ya yi mataimakin shugaban kasa, idan Allah ya sa an zabe ni, to zan cika burin da na ke da shi na inganta tattalin arzikin Najeriya, ta yadda za ta zama kasa mai karfin tattalin arzikin da kowa zai so ya shigo ya zuba jari.
“Amma tsarin Babban Bankin Najeriya, CBN wajen tsadar musayar kudaden kasashen waje, ya na sa masu zuba jari daga waje su na kaurace wa Najeriya. Wanda kuma ba haka ya kasance ya zama ba.”