Najeriya za ta ciyo bashin dala miliyan 300 don kawar da zazzabin cizon sauro

0

Gwamnatin Najeriya ta amince ta ciyo bashin dala miliyan 300 daga bankin Musulunci ‘Islamic Development Bank’ da bankin raya kasashen Afrika, ‘African Development Bank’ don kawar da zazzabin cizon sauro a kasar nan kwata-kwata.

Najeriya ta bayyana haka ne a taron samun madafa kan cutar a taron kasashen nahiyar Afrika da aka yi a kasar Tanzania.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi amfani da wadannan kudade (dala miliyan 300) da gudunmawar dala miliyan 18.7 da ta samu wajen raba gidajen sauro da ya kai miliyan 15 wa mutane kyauta sannan da bunkasa sarrafa magugunan cutar da kamfanonin sarrafa magani a kasar ke yi.

Share.

game da Author