Wata likita da ta kware a kimiyyar warkar da cutukan da ya shafi jijiya Njideka Okubadejo ta bayyana cewa a cikin mintuna biyu cutar dake shanye bangaren jikin mutum na kashe mutum daya cikin mutane biyu a Najeriya.
Likitan ta bayyana haka ne a jawabin da ta yi a jami’ar jihar Lagas game da ilolin da cutar ke yi a jikin mutum.
Ta ce mutum kan kamu da wannan cutar ne idan jini baya haurawa kwakwalwa yadda ya kamata.
Ta kuma ce idan har ba a gaggauta neman magani ba cutar na iya yin ajalin mutum.
A karshe Okubadejo ta ce bincike ya nuna cewa cutar kan yi ajalin mutane 120 zuwa 240 a cikin mutane 100,000 a Najeriya.
” Sanin kowa ne cewa adadin yawan mutanen kasar nan ya kai miliyan 184 wanda idan aka kwatanta yawan mutanen dake mutuwa sanadiyyar wannan cutar za a ga cewa mutane 281,520 ke mutuwa duk shekara.”
Discussion about this post