Kotu ta hana Gwamnati sake bayyana sunan Secondus a cikin barayin kudin Najeriya

0

Babbar Kotun Jihar Ribas ta hana Gwamnatin Tarayya, Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ko ma wani ejan na gwamnati lissafawa har da sunan Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus a cikin sunayen wadanda Gwamnatin ta ce sun wawuri kudin kasar nan.

Babban Alkalin Jihar, A. I. Iyayi-Lamikanra ne ya bada wannan umarnin a Fatakwal jiya Litinin a lokacin da ya fara sauraren karar da Secondus ya maka gwamnatin tarayya da kuma minista Lai kotu. .

Secondus dai ya ce shi bai ci nanin ba, don haka ba zai zauna nanin ta bata masa suna a idon jama’a ba, dalili kenan ya garzaya kotu.

Idan ba a manta ba, a lokacin mulkin Umaru ‘Yar’Adua, EFCC a karkashin Nuhu Ribadu sun lissafa jerin wasu mutane sama da 100 da ake zargin sun ci kudin Najeriya.

Amma a lokacin Lai Mohammed na a sahun gaba wajen masu cewa bai kamata EFCC ta yi haka ba, tauye hakkin jama’a ne.

A yau kuma Lai shi ne mai bayyana sunaye, har da na wadanda shari’ar su ta na kotu.

Lauyoyin Secondus Emeka Okpoko da Emeka Echezona ne suka shigar da karar a madadin shugaban jam’iyyar PDP din, Uche Secondus.

Tun ranar 6 Ga Afrilu ne kotun ta bada umarnin cewa mai korafin na ‘yancin a saurare shi, kuma ya ce a aika wa gwamnati da Lai sammace.

An daga shari’ar zuwa 28 Ga Mayu, 2018 domin ci gaba da sauraren bayanan hujjoji daga kowane bangare.

Share.

game da Author