A ranar Lahadi ne gwamnatin tarayya ta yi kira ga mutane da a daina Zubar da Ledoji da fasassun robobi a ko-ina cewa hakan na lalata wuraren zaman mu ne da muhallin mu.
Ministan muhalli Ibrahim Jibril ya bayyana da haka a Abuja a taron kare muhalli wanda ake yi ranar 22 ga watan Afrilu na kowane shekara.
Jibril ya bayyana cewa hakan na lalata muhalli sannan yakan zamo illa ga lafiyar mu.