Iyayen ‘yan matan Chibok sun yi hadari a hanyar Song zuwa Yola

0

Kakakin kungiyar iyayen ‘yan matan Chibok Ayuba Alamson ya bayyana cewa wasu daga cikin iyayen ‘yan matan sakandare na Chibok sun yi hadarin mota ranar Lahadi da karfe 10 na safe a hanyar Song zuwa Yola, Jihar Adamawa.

Alamson ya ce sun yi hadarin ne a hanyar su na zuwa taron iyaye na jami’ar ‘American University of Nigeria (AUN) dake Yola.

” Sanadiyyar wannan hadarin mutum daya ya rasu sannan wasu 17 sun sami raunuka.”

A karshe tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a shafinsa na Tiwita ya jajanta musu.

Share.

game da Author