Jami’an tsaro sun saki Dino Melaye

0

Bayan ‘yar gajeruwar bincike da akayi wa sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja, jami’an tsaron sun sake shi.

Ko da yake dukkan su jami’an tsaron da suka damke Sanata Dino sun shiga cikin rudani bayan jami’an ‘yan sanda sun kasa tabbatar da cewa lallai an yi shelar kama sa duk inda aka gansa. Sun yi cirko-cirko a gaban sanatan bayan sun yi ta neman dalilin dakatar da shi a filin jirgin saman.

Daga baya dai da suka kasa bayyana wata hujja da ke nuna rundunar ‘yan sanda na neman sa ruwa a jallo sai suka sake sa.

Idan ba a manta ba da safiyar yau Litinin ce Sanata Dino Melaye ya bayyana a shafin sa na tiwita cewa ‘yan sandan Najeriya sun cafke shi a lokacinn da ya ke kokarin tafiya kasar Morocco domin halartar wani taro.

Ya ce an cafke shi bayan ya kammala hidindimu a cikin filin jirgin saman Nnamdin Azikwe da ke Abuja, a lokacin da ya ke kokarin ya tafi ya hau jirgi.

Tun cikin watan da ya gabata jami’an tsaro suka bada sanarwar cigiyar neman sa da ake yi dangane da binciken da ake a kan sa na wata shari’a wadda a yanzu haka ta na kotun Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Neman da ake yi masa na da nasaba da zargin hannun da ya ke da shi a wani kisan kai, da kuma ikirarin da wasu mahara suka yi cewa shi ne ke ba su makamai.

Share.

game da Author