Wamakko ya karyata labarin gayyata daga EFCC

0

Tsohon Gawamnan Jihar Sakoto, Sanata Aliyu Wamakko, ya karyata maganganun da aka rika yadawa cewa EFCC ta aika masa da takardar gayyata da ya kai kan sa a yi masa wasu tamabayoyi.

Wamakko ya bayyana wa manema labarai a Sokoto cewa labaran wadanda aka rika watsawa a makon jiya, na bogi ne, kuma kirkira ce daga masu neman sa da sharri domin su bata masa suna.

“A fili ta ke cewa jama’a sun san irin rayuwar da na yi, tun ina malamin makaranta har na zama gwamna, har zuwa mukamin da na ke yanzu, ba canjawa na yi ba.

“Ga Allah kadai na dogara, domin shi kadai ke bada mulki ga wanda ya ke so ya bai wa. Kuma shi ne ya daukaka darajar siyasa ta zuwa matakin da na ke a yanzu. Don haka na yi amanna cewa Allah ne kadai zai iya kaskantar da ni, amma ba wani mutum mai gaba da ni ba.” Inji Wamakko.

“Wasu dibgaggun magauta ne kawai da ba su iya fitowa fili su tunkare mu, sai suka yi amfani da sunayen karya suka danganta ni da Sanata Rabi’u Kwankwaso wai mun yi tabargazar naira biliyan 18 a lokacin da mu ke gwamna.”

Daga nan sai ya ce ba EFCC ce ta fitar da korafin da ake yi akan mu ba, wasu masharranta ne kawai. Ya na mai cewa EFCC hukuma ce da ta san yakamata, kuma ba za ta taba rubuta kalamai irin na zancen ‘yan-tasha a cikin wasikar da za ta gayyaci wanda ta ke zargi, kamar yadda aka yi amfani a cikin waccan takardar ba.

Wamakko ya kara da cewa tara dimbin dukiya da tabargaza ba dabi’ar sa ba ce. “Tun da na hau gwamna ba na ko tafiye-tafiye zuwa kasashen waje. Sau daya na taba zuwa Amurka da kuma Ingila, shi ma gayyata ce aka yi min, ba bushasha ko gantali ya kai ni ba.”

Wamakko ya zayyano wasu ayyuka da yayi a lokacin yana gwamnan jihar Sokoto wanda ya ce sunanan mutanen jihar na mora har yanzu.

A karshe ya ce ba shi da wata matsala da Shugaba Muhammadu Buhari.

Share.

game da Author