Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya ziyarci Sandra Davou da aka make lokacin da masu satar sandar iko suka far wa majalisar.
Ko da yake Saraki ba ya Kasar lokacin da hakan ya faru, ya garzaya har gidan Sandara dake Bwari tare da makarraban sa domin duba jikin ta.
Ya jinjina wa Sandra kan kokarin da tayi na kokuwa da masu sace sandar inda har ta ji rauni.
Idan ba a manta wasu ‘yan ta’adda sun far wa majalisar Dattawa ranar Larabar da ta wuce, inda suka dauke sandar Iko na majalisar a idanuwar kowa.
Mutane da dama sun yi tir da wannan abu da ya faru, sannan sun yi kira ga jami’an tsaro da su tabbata sun taso keyan wadanda suka aikata haka.