‘Yan kunar bakin wake sun kashe wasu masallata a Bama

0

Wasu mata dauke da bam sun kashe kan su da wasu masallata biyu bayan sun tada bam a daidai ana sallar Asuba a garin Bama jihar Barno.

Wani mazaunin unguwar ya ce bayan mutane biyun da suka kashe akalla mutane 8 sun sami raunuka.

Bama dai na daga cikin garuruwan da suka fi fama da hare-haren Boko Haram a jihar Barno.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar wannan hari a wata takarda da kakakin rundunar ya fitar yana bayanin abin da ya faru.

Share.

game da Author