A biya mu kudin Sallamar mu kawai, ba horo don a bamu bashi muke so ba- korarrun Malaman Kaduna

0

Malaman makarantun firamaren Jihar Kaduna da gwamnatin Jihar ta kora bayan fadi jarabawar gwaji sun kalubalanci gwamnatin jihar da ta dakatar da shirin horas da su sana’o’i da ta shirya, cewa tunda ya kore su, ya basu kudin sallamar su kawai su kara gaba.

Korarrun malamai sun bayyana haka ne a Zariya bayan sun halarta a makarantar Alhuda-Alhuda domin ganawa da jami’an gwamnati.

Jami’an gwamnati sun ziyarci Zariya ne domin horas da malaman da gwamnati ta kora na Kananan hukumomin Zaria, Soba, Giwa, da Sabongari.

Jami’an sun ce sun tara tsoffin malaman ne domin su horas dasu sana’oin hannu cewa gwamnati na shirin basu bashi domin su kama Sana’a.

Duk malaman da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Zariya sun ce ba haka gwamna yayi da su ba.

” Idan ba wata sabuwar yaudara ba, bayan gwamna da kansa ya ce zai biya mu kudin sallama, me ya kawo maganar horas da mu sana’a. Idan za a biya mu a biya mu kawai mu san inda dare yayi mana tun da an riga an kore mu.

” Wannan Abu da akayi mana ba mu ji dadin Shi ba. Ta yaya za a ce wai sai bayan mun tattara a nan muna jiran a biya mu kudin sallama kawai sai a bige da cewa wai horo za a bamu Sannan a bamu bashi. Kawai a biya mu mu san inda dare yayi mana.

Malaman dai sun ki sauraran jami’an gwamnati, sannan sun yi watsi da wannan shiri na gwamnati.

Share.

game da Author