Mahara sun kashe mutane da dama a Zamfara

0

A ranar Juma’a ne mazaunan kauyen Kabaro dake karamar hukumar Maru jihar Zamfara da rundunar ‘yan sandan jihar suka tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa wasu mahara sun far wa kauyuka uku a Jihar.

Mazauna kauyukan bayyana cewa maharan sun kai wa kaukan Kabaro, Danmani Hausawa da Danmani Dakarkari hari sannan babu wanda ke da masaniyyar adadin yawan rayukan da aka rasa sanadiyyar wannan hari.

PREMIUM TIMES ta gana da wani mazaunin karamar hukumar Maru wanda ya bayyana cewa maharan sun fara kai hari ne a kauyen Kabaro ranar Alhamis da yamma sannan washe gari suka far wa kauyukan Damani Hausawa da Damani Dankarkari.

” Maharan sun far ma wadannan kauyuka ne haka kawai, Sannan basu bar duk Wanda suka yi Karo da ba ko su hallaka shi, ko ya tsira da rauni.

A karshe kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Shehu Mohammed ya tabbatar wa mutanen garin cewa za su yi iya kokarin su wajen kare rayukan mutane sannan sun fara gudanar da bincike domin kamo maharan.

Share.

game da Author