Dalilan da ka Iya kayar da APC a 2019

0

Matsalolin da APC ke fama da su, za su iya zama babbar matsala ga jam’iyyar idan zaben 2019 ya zo.

Tabarbarewar tsaro a Arewacin kasar nan ya yi muni, ta inda har kauyuka masu garkuwa da mutane ke bi, su na sallama gidaje kon su kutsa kais u sungumi maigida ko amarya ko uwargida, da rana tsaka.

Ba ka taba mallakar naira dubu 200 ba, amma a ce sai an biya naira milyan biyar za a sake ka.Wannan zai zame wa APC ko Buhari alakakai a zaben 2019.

Maganar gaskiya wadannan matsaloli sun addabi mutane, kuma sun fara dawowa daga rakiyar wadanda suka kasa magance su.

Har yanzu gwamnatin APC dawurwura ta ke ta yi, duk wata matsalar da gwamnatin ta haifar, maimakon ta dauki laifi sai ta dora laifin a gwamnatin baya. Wannan ma jama’a da dama sun fara gajiya da kullum ana ba su uzuri.

Matsalar tattalin arziki da ake ta shelar cewa an ci gaba, har yanzu talaka dai abubuwa a rayuwar sa sai ta’azzzara su ke yi. Abincin da gwamnatin APC ke tutiyar ana nomawa, har yau farashin sa bai sauko ba a garuruwa. A kauyuka banda kukan talauci da rashin sukunin wadata iyali da abinci babu abin da ake yi.

Jami’an kwastan na kara janyo wa gwamnatin APC bakin jini, ta yadda suke bin masu fasa-kwaurin shinkafa ko da a kan babur ka shigo da buhu biyu, ta a kan iyakar Najeriya, idan ka ki tsayawa, tirka maka bindiga za su yi. Kuma duk wanda suka kashe, shikenan alkiyamar sa ta tsaya kenan, sai dai a haifi wani. Akwai ma lokacin da suka shiga har cikin birnin Katsina suna dirka wa jama’a harbi.

Farashin fetur da aka yi alkawarin zai sauko, sai ma hauhawa ya yi, yayin da dalar Amurka da Buhari ya yi alkawarin zai sauko da ita daidai da naira, ita ma abin ya zama tatsuniya, har ma kamar an hakura kawai.

Irin yadda ake yayin guguwar Buhari a fadin kasar nan, a yanzu abin ya ragu matuka. Lokacin da ya sake bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takara a zaben 2019 mai zuwa, an yi tunanin za a ga kasar nan an rikice da murna ko’ina, amma banda Kano da wasu tsiraru suka fita kan titi, duk kasar nan shiru ka ke ji.

Irin yadda da dama daga cikin wadanda suka goyi bayan Buhari a zaben 2015, amma a yanzu suka dawo su na caccakar gwamnatin sa a soshiyal midiya, hakan na nuni da cewa da yawa a zaben 2019 ba za su wahalar da kan su a kan zaben APC ba.

A zaben 2015 gaba daya kuri’un da aka yi wa PDP rata da su ba su kai milyan 3 ba, duk kuma da irin tirnikewar da guguwar Buhariyya ta yi. Don haka idan aka yi la’akari da yadda gwamnatin APC ke da bakin jini a Filato, Benuwai, Taraba da kuma uwa-uba ga bangaren ‘yan Kwankwasiyya a Kano da fadin kasar nan, to za a fahimci da wuya a 2019 APC ta yi irin tasiri, cara da kuma guguwar da ta yi a 2015.

Irin yadda musamman a Arewa aka dawo rakiyar wasu gwamnoni da dama, musamman a Kano, Kaduna da Zamfara, da kuma sanatoci da ‘yan majalisun tarayya, zai yi wuya APC ta sake samun kuri’un da ta samu a Arewa, musamman a yankin ‘Middle Belt’ da aka sani da Arewa ta Tsakiya.

Layar asirin nan ko kuma lakanin cin zaben nan a saukake da ake kira ‘Sak’, tuni aka karya lagon sa. A yanzu kowa ya san cewa a 2019 wani ba zai ci arzikin wani ba, kowa ta sa ta fisshe shi kawai. ‘Nafsi-nafsi’ kenan kamar yadda a yanzu za ka rika jin masu jin haushin wakilan su na furtawa.

Rikicin cikin jam’iyyar APC da har yanzu babu ranar shawo kan sa sai ma kara muni da ya ke yi, wannan ma zai kara gurgunta jam’iyyar. Sai dai kuma masu yaudarar kan su na ganin kamar abin ba zai iya gurgunta APC ba. Zai yi wuyar gaske Kwankwasawa su jefa wa Buhariyya kuri’a.

Idan ta yi zafi ma, to ‘ant-party’ za su yi. Haka a Kaduna, dimbin wadanda Gwamna Nasir El-Rufai ya musguna wa da su da magoya bayan su, da sauran ‘wa gairahum’ da suka gaji da mulkin sa, ko an hada su da Allah su zabi APC, to ba za su zabe ta ba, sai dai a yi ragas, kowa ma rasa kenan.

Jama’a da dama a Kano da Sakkwato da Bauchi inda aka zuba wa Buhari ruwan kuri’u, sun a jin haushin wahalar da suka sha a 2014, amma har yanzu ba su ga wani abin a zo a gani daga gwamnatin tarayya ba. Abin da ya fi bai wa Kanawa da jama’ar Bauchi haushi, shi ne a rasa abin da za su mora har zuwa yansu sai

gidajen kurkuku.

Share.

game da Author