Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Geidam ya bayyana cewa tun da Mustapha Maihaja ya dare kujeran shugabancin hukumar bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) jihar Yobe ba sake samun tallafi daga hukumar NEMA ba ko da sau daya ne kuwa.
Geidam ya fadi haka ne a wata wasika da ya aika wa kwamitin bada agaji na majalisar wakilai.
Kwamishinan ilimi Ibrahim Lamin ne ya gabatar da wannan wasika.
” Sanin kowa ne cewa jihar Yobe na daya daga cikin jihohin yankin arewa maso gabashin kasar nan da suka yi fama da hare-haren Boko Haram. Amma tun da Maihaja ya canji Sidi a hukumar NEMA, ya katse Yobe daga lissafin sa.”
Shugaban NEMA, Maihaja da yake amsa tambayoyi game da haka a gaban kwamitin ya bayyana cewa ba shi da masaniya abubuwan da ake zargn sa akai.
” Ni dai na san na bada umarnin a raba kayan tallafi ga duk jihohin da ke bukata. Ba zan iya sanin ko an kai ba ko a’a.”
Shugaban kwamitin Ali Isa (PDP Gombe) ya umarci Maihaja da ya gabatar da hujjojin da zai nuna cewa lalle ya yi rabon da jihar Yobe ranar Talata.
A karshe Ali Isa ya kuma umurci Maihaja da ya dawo da darektoci shida da ya dakatar domin kwamitin ta gano cewa an yanke musu hukunci ba tare da an basu damar kare kan su ba.
Darektocin da aka dakatar sun hada da Akinbola Gbolahan, Umesi Emenike, Mallam Alhassan Nuhu, Mamman Ali Ibrahim, Ganiyu Yunusa Deji da Kanar Mohammed.