Gwamnatin jihar Anambra na shirin yi wa yara miliyan 1.16 a jihar allurar rigakafin cutar Shan inna a cikin watan Afrilu.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Joe Akabuike ya sanar da haka wa manema labarai ranar Alhamis a Awka.
Ya ce za a fara karon farko ranar 21 ga watan Afrilu sannan suna sa ran za su yi wa yara 233,005 allurar rigakafi cikin kwanaki hudu kamar yadda suka tsara.
Akabuike ya ce ma’aikatan su za su zazzaga gidaje, makarantu da wuraren ibada domin yi wa yara ‘yan watanni tara zuwa shekara biyar allurar.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su gabatar da ‘ya’yan su domin ayi musu alluran.
” Za mu zage damtse wajen wayar da kan mutane musamman iyaye kan mahimmancin yi wa ya’yan su allurar rigakafi.
A karshe Akabuike ya ce yajin aikin da kungiyar JOHESU ke yi ba zai hana su yin wannan aiki ba.