Tir da abin da ya faru a majalisa – Balarabe Musa, Saraki, Dogara, ‘yan Najeriya

0

Bayan sa’o’I kadan da bayyana sace sandar ikon Majalisar Tarayya, Tsohon Gwamnan farar hula na Jihar Kaduna a Jamhuriya ta Biyu, Balarabe Musa, ya bayyana mamaki da al’ajabin sa dangane da sace sandar da aka yi.

Da ake hira da shi ta wayar tarho, dattijon yace wannan cin mutunci ne ga Majalisar Tarayya, kuma babbar barazana ce ga su ‘yan majalisar da sauran jama’a.

Ya ce muddun har ‘yan iska za su kutsa kai tsaye cikin majalisa da rana tsaka su sace sandar majalisa, to tabbas rashin tsaro a kasar nan ya kai makura.

SARAKI DA DOGARA SUN LA’ANCI YUNKURIN

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, duk sun yi tir da wannan shigar-kutse da aka yi aka sace sandar mulki a majalisar dattawa. Su biyun duk sun nuna cewa babu wata barazana da za a yi wa Majalisa har a karkatar da ita daga aikin ta da ta sa a gaba.

Haka suma jam’iyya mai mulki da jam’iyyr adawa duk dun la’anci wannan abu da ya faru a zauren majalisar.

MATAIMAKIN SHUGABA YA BAI WA JAMI’AN TSARO WA’ADI

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, shi ma ya nuna bacin ran sa matuka dangane da abin da ya faru.

“Wannan abu da ya faru abin takaici ne kuma cin mutunci ne. Na kira Shugaban Majalisar Dattawa, kuma ya ce min kada mu sake mu soke zaman majalisa na yau, saboda wannan farmaki da aka kawo mana. Y a ce min idan muka soke zaman yau, to an yi galaba a kan mu, kuma an yi galaba a kan dimokradiyya kenan.

“Saboda haka za mu ci gaba da zaman mu nay au ba za mu fasa ba. Haka kuma ina sanar da cewa Majalisar Dattawa ta bai wa ‘yan sanda da SSS awa 24 su je duk inda za su gano mana sanadar ikon majalisa su dawo mana da ita.”

GBAJABIAMILA: AN KUNYATA MAJALISA A GABAN BAKI

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, ya bayyana takaicin sa ganin yadda wasu ‘yan takife suka kutsa cikin Majalisar suka sace sandar mulki. Da ya ke jawabi a lokacin da suka shiga zauren majalisar dattawa domin su yi jaje, ya bayyana cewa an tozarta majaliasr Najeriya, domin hakan ya faru ne a lokacin da Shugabannin Majalisar kasar Gambiya suka kawo ziyarar gani-da-ido domin su ga yadda Majalisar Najeriya ke gabatar da zaman su.

SANATA WAKU YA CE YUNKURIN JUYIN MULKI NE

Tsohon Sanata Waku, ya bayyana abin da ya faru a Majalisar Dattawa da cewa ba shi da wani bambanci da yunkurin juyin mulki, kuma bain bakin ciki da damuwa ne, kuma barazana ce ga tsaro a kasar nan.

SANATA BEN BRUCE

Maganar gaskiya Sanata Omo Agege bai kyauta ba, domin idan aka dubi abin nan a hankalice, ai an dakatar da shi, kuma har ya garzaya kotu. Kai ko da ma bai je kotu ba, ai bai kamata ya shigo zauren majalisa ba. Sannan tunda ma har ya kai kara kotu, to don me zai shigo majalisa alhali kotu ba ta yanke hukunci ba? Kuma maimakon ya shigo shi kadai, sai ya shigo tare da ‘yan takife.

BAN SHIGO DA ‘YAN-TA-KIFE BA –Omo Agege

Sanata Omo-Agege ya karyata cewa shi ne ya dauki nauyin wasu ‘yan nta0kife da suka kutsa cikin zauren majalisa har suka sace sandar iko. A cikin wata takarda da kakakin sa ya fitar, Omo-Agege ya bayyana cewa shi kadai ya shigo majalisa bai shigo tare da wasu ‘yan takife ba. Sannan kuma ya goyi bayan a yi bincike domin a gano inda gaskiyar ta ke.

RA’AYOYIN JAMA’A

Jama’a da daman a tofa albarkacin abin da bakin su zai iya furtawa dandagane da wannan mummunan lamari da ya faru a majalisar Najeriya. Akasari an fi nuna damuwa da sakacin jamai’an tsaro da har suka bari wasu karti suka shiga har cikin zauren majalisar.

Wasu na ganin cewa idan har duk da irin tsaron da ake nunawa Majalisar Tarayya kuma haka ta faru, to idan ba a yin hankali ba wasu mugaye za su iya shiga su illata ‘yan majalisa kai tsaye.

Sai dai kuma akwai masu cewa shirin gaba daya wasan kwaikwayo ne domin a hana majalisar dattawa tilasta sauya ranakun zabe. Su na ganin gwamnati ce ta ingizo ‘yan ta-kifen, domin bayan an tashi hankulan Majalisar Dattawa, sai ga shi gaba dayan su sun nuna gajiya da ci gaba da tattauna batun sauyin sunayaen.

AN GANO SANDAR MULKI A KARKASHIN GADA

Rundunar ‘yan sandan Abuja ta bayyana cewa ta gano sandar mulkin da aka sace a karkashin wata gada, bayan da wasu ‘yan ta-kife suka kutsa cikin majalisa, suka sace ta. An ce sun tsinci sandar ne a karkashin gada a kan hanyar fita Abuja nufi filin jirgin sama.

KARIN HASKE

Tuni dai Mataimakin SHugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu ya gana da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo inda ya yi masa bayanin abin da ya faru a majalisa. Ya gana da shi ne saboda Shgaba Muhammdu Buhari bay a kasar. Shi ma Ekweremadu ya yi shugabancin majalisar ne a ranar da abin ya faru, saboda Saraki ba ya kasar.

Share.

game da Author