Shugaban hukumar kula da kiwon lafiya na babban birnin tarayya Abuja Humphrey Okoroukwu ya bayyana cewa cikin mutane uku da suka kamu da zazzabin Lassa, biyu sun rasu.
Ya fadi haka ne da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
A hirar, ya kara da cewa sun tabbatar da haka ne bayan kammala gwaji kan wasu mutane 38 da ake zargin sun kamu da cutar.
” Bayan mun gwada su sai muka gano cewa mutum uku cikin su na ke dauke da cutar sai dai biyu daga ciki sun rasu bayan dan wani lokaci.
Okoroukwu ya ce asibiti ta sallami wannan mutum da yake samun kula a asibitin bayan sun tabbatar da ya samu lafiya.
A karshe ya yi kira ga mutane da su mai da hankali wajen tsaftace jiki, abinci da muhallin su sannan a gaggauta zuwa asibiti a duk lokacin da aka kamu da zazzabi.