Na ba da madaurin kwankwaso na ‘ Belt’ domin ya zama sandar mulki a majalisa – Shehu Sani

0

Sanata dake wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya ce ya bada gudunmuwar madaurin kwankwason sa wato ‘Belt’ a majalisa a madadin sandar Mulki da aka dauke da karfin tsiya a majalisar.

Sanin kowa ne cewa muddun babu wannan sanda, zaman majalisar ba zai yiwu ba.

Shehu Sani ya bayyana cewa yayi haka ne domin a ci gaba da zaman majalisar, sannan kuma wasu daga cikin sanatocin sun amince a lokacin da ya mika wannan belt nasa.

Kafin a shimfida wannan ‘belt’ ne fa sai aka taho da wani sandar mulkin a madadin wanda a aka tafi da shi.

Idan ba a manta ba, a safiyar Larabar yau ne wasu da ake zaton na tare da sanata Omo-Agege suka far wa majalisar dattawa da karfin tsiya suka dauke wannan sanda.

Share.

game da Author