Wasu likitoci dake jami’ar Melbourne dake jihar Victoria a kasar Australia sun bayyana cewa wata cutr dake cin fata da naman jikin mutum ta bullo a kasar.
Shugaban likitocin Daniel O’Brien ya ce ita dai cutar wanda ake kira ‘Buruli ko Daintree’ cuta ce dake fitowa a jikin mutum kamar gyambo wanda kan cinye fatar jiki sannan idan ba a gaggauta neman magani ba ko kuma hanyar dakile yaduwar ta, ta kan sa a yanke wani bangare na jikin mutum ko kuma ya to ajalin sa.
” Cutar ta fara bullowa ne a kasar mu a shekarar 2016 inda mutane 182 suka kamu da cutar, a shekarar 2017 mutane 275 sun kamu sannan a wannan shekaran mutane 30 ne ke dauke da cutar.
Daniel ya ce rashin iya gano yadda ake kamuwa da cutar na matukar ci masu tuwo a kwarya.
Ya ce sanadiyyar wannan matsalar basu na yi game da yadda mutum zai iya kare kansa daga kamuwa da cutar da kuma yadda ake iya kamuwa da ita.