Za mu sarrafa sabon maganin zazzabin cizon sauro – kungiyar MMV

0

Kungiyar ‘Medicines for Malaria Ventures’ (MMV) ta bayyana cewa za ta hada hannu da wasu kungiyoyi don sarrafa maganin da zai taimaka wajen kashe kwayoyin cutar zazzabin cizon sauron da basu jin magani.

Kungiyar ta ce haka zai taimaka wajen rage matsalolin da ake fama da su wajen shawo kan yaduwar cutar.

” Wannan shawara da muka dauka ya kunshi gudanar da bincike da sarrafa maganin don amfanin mutane.”

Bayanai su nuna cewa jihar Barno a Najeriya ta yi fama da cutar zazzabin cizon sauro sanadiyyar aiyukan Boko Haram na tsawon shekaru takwas.

” Rashin samun asibitoci da matsuguni da mazauna jihar Barno suka yi fama da su sanadiyyar aiyukan Boko Haram na cikin dalilan da ya sa zazzabin cizon sauro ya addabi mutanen yankin.”

A karshe bisa ga rahotan ‘World Malaria Report’ mutane miliyan 216 sun kamu da cutar a shekarar 2016 daga miliyan 211 da suka kamu da cutar a 2015.

Sannan a shekarar 2016 cutar ta yi ajalin mutane 445,000 daga mutane 438,000 da suka rasu sanadiyyar cutar a shekarar 2015.

” Kashi 90 bisa 100 na mutanen da suke rasa rayukan su sanadiyyar cutar zazzabin cizon sauro daga yankin kudu da Saharan Afrika ne sannan yara kanana na rasa rayukan su a cikin mintuna biyu a dalilin kamuwa da zazzabin cizon sauro.”

Share.

game da Author